Haiti


Mahalarta taron tuntuɓar Haiti sun haɗa hannu. Tattaunawar ta tattaro wasu shugabannin coci 30 na Haiti da shugabanni a aikin Kiwon Lafiyar Haiti tare da ’yan’uwa ’yan Amirka kusan 20 da shugabanni daga Amirka da suke hidima a Haiti.
Hoton Bob Dell.

Eglise des Freres a Haiti (Cocin ’yan’uwa da ke Haiti) ’yan’uwan Haiti da ke zaune a Amurka ne suka soma. ’Yan’uwa na farko sun yi baftisma a Haiti a watan Mayu 2003. Ya zuwa 2020, akwai mutane fiye da 3000 a majami’u 21 da wuraren wa’azi takwas tare da naɗaɗɗen masu hidima 16.

Ma’aikatar Bala’i ta ’yan’uwa ta jagoranci taimakon Cocin ’yan’uwa bayan guguwar Gustav, Hanna, da Ike da kuma girgizar ƙasa na Janairu 2010, waɗanda dukansu suka jawo babbar barna a ƙasar da ta riga ta kasance matalauta.

Bayanai kan Haiti Medical Project